IQNA

Wasu Labarai sun Ce An Kama Dan Gaddafi A Yakin Da Ake Yi A Libya

17:13 - August 23, 2011
Lambar Labari: 2175715
Bangaren kasa da kasa, wasu rahotanni da kafofin yada labaran kasashen yammacin turai suka watsa dangane da kame dan shugaban kasar Libya Saiful Islam Gaddafi, sai dai kuma daga bisani ya bayyana a cikin birnin Tripoli yana yawo hankalinsa kwance.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin in Aljazeera an bayyana cewa, wasu rahotanni da kafofin yada labaran kasashen yammacin turai suka watsa dangane da kame dan shugaban kasar Libya Saiful Islam Gaddafi, sai dai kuma daga bisani ya bayyana a cikin babban birnin kasaryana yawo hankalinsa kwance kamar dai yadda ake iya gani daga fuskarsa da kuma yanayin da yake ciki.

Dan shugaban kasar Libya Saiful Islamil-Kaddafi wanda 'yan tawayen kasar suka ce sun kama a daren shekaranjiya lahadi ya sake bayyana a gaban manema labarai a cikin daren da yagabata inda ya musanta ikirarin na 'yan tawaye, yana mai cewa birnin Tripoli na karkashin ikon sojoji masu biyayya ga mahaifinsa bayan da suka karya lagon 'yan tawaye da suka shiga a ranar lahadin da ta gabata.
Saifil Islam ya ce kasashen yamma wadanda ke mara wa 'yan tawaye baya domin wawashe arzikin kasar, sun amfani da fasahar zamani don lalata kafafen yada labarai na kasar, sannan kuma suna yada labaran karya masu cewa an kawo karshen gwamnatin mahaifinsa.

Dan na shugaba Kaddafi ya ce ko shakka babu 'yan tawayen masu samun goyon bayan kungiyar Nato sun samu nasarar kutsawa tare da kama wasu muhimman wurare aTripoli, to amma wannan ba ya nufin cewa sun samu nasara domin kuwa al'ummar Libya na tare da mahaifinsa a cewarsa.

847809

captcha