Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na jaridar Yaum Sabi ta kasar Masar cewa, rahotannin da wasu kafofin yada labarai suke watsawa dangane da makomar shugabn kasar Libya Mu'ammar gaddafi na nuni da cewa ya gudu zuwa yankin Sabha da ke cikin kasar bayan da 'yan tawaye dauke da makamai suka shigo cikin birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libya.
Yan tawayen kasar Libya sun bada labarin kwace iko da babban filin sauka da tashin jiragen sama na babban birnin kasar Tripoli.
Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ne ya bayyana wannan labarin a daren jiya asabar, kuma ya kara da cewa ana jin karar tashin boma bomai da kuma aman wutan bindigogi a kusan ko ina a cikin birnin.
Labarin ya kara da cewa tun lokacinda yan tawayen suka sami iko da garin Zawiyya mai muhimmanci, sojojin kazzafi basa nuna wata turjiya mai yawa a gaban yan tawayen sai su gudu.
A farko farkon tawayen dai, a cikin watan Febreru da ya gabata, mutanen garin Zawiyya sun gudanar da zanga zangar nuna kiyayya ga mulkin shugaba Gazzafi amma sojojinsa suka murkushesu da manyan bindigogi.
Har'ila yau garin Zawiyya ce kadai babban hanyar fita daga kasar ta kan iyakarta da kasar Tunisia. Kuma tana da babban matatar mai wanda ke bada makamaci mai yawa ga babban birnin kasar.
Har'ila yau a wani labarin kuma gwamnatin kasar Tunisia ta amince komitin gudanarwa na yan tawayen kasar ta Libya mai mazauni a birnin Bengazi a matsayin halattaciyar gwamnatin kasar ta Libya a jiya asabar.
847812