Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, daga cikin irin bayanan da ake ta watsawa a kasashen duniya, yanzu an fara shirin gudanar da taruka da kuma gangami na ranar Qods a sassa na kasashen musulmi da ma wasu kasashen da ba na musulmi ba, wanda zai gudana gobe Juma'a ta karshen watan Ramadan mai alfarma kamar yadda mariyagayi Imam Khomeini (RA) ya ayyana a lokacin da yake raye, kuma tun daga lokacin ne ake gudanar da tarukan wanna rana mai albarka.
Juyin juya halin muslunci na Iran wanda ya kasance tun kimanin shekaru talatin da uku da suka gabata, ya yi babban tasiri wajen fadakar da al'ummar musulmi dangane da halin da ake ciki na zaluncin kasashe masu girman kai, da kuma munafukai daga cikin geamnatocin kasashen musulmi da na larabawa.
Wannan na daga cikin muhimamn abubuwa da wannan juyin juya hali ya gadawar al'ummar musulmi, musamman ma wadanda ake zalunta daga cikinsu, kuma amfanin hakan zai koma ne ga dukkanin al'ummomi, musulmi da wadanda ba musulmi bad a suke fuskatar zalunci daga kasashen duniya masu girman kai da kuma munafukai.
Fara shirin gudanar da taruka da kuma gangami na ranar Qods a sassa na kasashen musulmi da ma wasu kasashen da ba na musulmi ba, wanda zai gudana gobe Juma'a ta karshen watan Ramadan mai alfarma kamar yadda mariyagayi Imam Khomeini (RA) ya ayyana tun sama da shekaru kusan talatin da suka gabata. 849117