IQNA

Palastinu Ta Zama Abun Yin Layya Ga Yahudawan Sahyuniya

10:55 - August 25, 2011
Lambar Labari: 2176574
Bangaren kasa da kasa, Palastinu ta zama abun yin layya ga yahudawan sahyuniya inda suka mamaye yankunan larabawa da kuma muhimman wurare na tarihin musulunci, da hakan ke nuni da irin mawiyacin halin da al'ummar musulmin yankin ta samu kanta a ciki.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din al-alam an bayyana cewa, Palastinu ta zama abun yin layya ga yahudawan sahyuniya inda suka mamaye yankunan larabawa da kuma muhimman wurare na tarihin musulunci, da hakan ke nuni da irin mawiyacin halin da al'ummar musulmin yankin ta samu kanta a ciki a wanna zamani da muke rayuwa wanda duniya ke ikirarin batun kare hakkin dan adam.

Babban jamii a hukumar Palasdinawa Sa'ib Uraykat ya bayyana fatar cewa akasarin kasashen duniya zasu goyi bayan bukatar Palasadinu na zama mambar Majalisar Dinkin Duniya a watan gobe.

Uryakat ya sheda wa wani kamfanin dilalncin labarai ta wayar tarho cewa: "Muna fatar sama da kasashe 150 zasu amince da kafuwar kasar Palasdinu a cikin iyakokin shekarar 1967 da gabashin birnin Kudus a matsayin fadar mulkinta."

A jiya Talata ne taron kungiyar kasashen Larabawa a birnin Doha ya tattauna batun neman taimakon kasashen duniya domin amincewa da kasar Palasdinu mai cikakken yanci wanda ake ganin cewa wasu daga cikin kasashen larabawan wadanda karnukan fararutar Amurka, mai yiwa suka kawo am shirin cikas.

Palasdinawan zasu gabatar da bukatarsu ga sakatare janar na Majalisa Dinkin Duniya Ban Ki Moon a ranar 20 ga watan Satumba a yayin da shugabannin kasashe zasu fara isa birnin domin halartan taron babban zauren karo na sittin da shida.

849082








captcha