Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na alqubanci an bayyana cewa, Sayyid Sadruddini Alqubanci babban limamin masallacin juma'a a birnin Najaf mai alfarma ya bayyana cewa komawar da mutanen Libya zsuka yi zuwa ga addini ita babban dalilin samun nasarrasu kan shugaban mulkin kama karya na kasar a borensu wanda ya kwashe tsawon watanni kimanin shida.
A bangare guda kuma an gano gawawwakin mutane hamsin da aka kona a cikin wani gidan kurkuku da ke kusa da Tripoli babban birnin kasar Libya,a jiya asabar ne majiyar yan tawayen Libya ta sanar da cewa an gano gawawwakin ne a yankin Salahud-Din mai nisan kilo mita biyar daga birnin Tripoli.
Rahonni na nuni da cewa mayakan da su ke biyayya ga hambararren shugaban kasar Mu'ammar Khaddafi ne da su ka sha kashi a hannun 'yan tawaye acikin wannan yankin su ka kona mutanen da su ke rike da su a yayinda su ke janyewa.
Daya daga cikin 'ya'yan Khaddafi mai suna Khamis wanda kuma kwamanda ne na rundunar soja mafi girma, sansaninsa ya kasance a cikin wannan yankin na Salahud-Din. kawo ya zuwa yanzu kaso 95% na birnin Tripoli yana hannun 'yan tawayen.
850444