IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Harin Abuja

14:02 - August 28, 2011
Lambar Labari: 2178074
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka dangane da harin ta'addanacin da aka kai birnin Abuja fadar mulkin kasar Nigeria a ranar juma'ar da ta gabata a kan babban ginin ofishin majalisar dinkin duniya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadrawa na OIC an bayyana cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka dangane da harin ta'addanacin da aka kai birnin Abuja fadar mulkin kasar Nigeria a ranar juma'ar da ta gabata a kan babban ginin ofishin majalisar dinkin duniya da ke cikin birnin.

tabbtar da mutuwar mutane 18 a wani harin da aka kaiwa ofishin majalisar dinkin duniya da ya ke a birnin Abuja, shedun ganin ido sun ce wata mota ce da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a babbar kofar shiga cikin ofishin abinda ya haddasa fashewa mai karfin gaske.

Wani ma'aikaci a ofishin mai suna micheal Osilaji ya ce ya ga gawawwaki masu yawan gaske a ko'ina, sai dai har yanzu da akwai wadanda su ke kwance a karkashin baraguzai, kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin amma jami'an tsaro sun fara nuna hannu ga kungiyar nan ta Boko Haram.

Wannan hari dai ya sanya shakku a cikin zukatan mutane da dama tarayyar Nigeria, domin kuwa ya z one a daidai lokacin da kasashen yammacin turai suke ta hankoron shigowa cikin kasar ba tare da wata matsala ba, amma babu hujjar yin hakan ba.

850238

captcha