IQNA

Musulmin Kasar Thailand Sun Zanga-Zangar La'antar Isra'ila

16:47 - August 28, 2011
Lambar Labari: 2178217
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Thailand sun yi wata gagarumar zanga-zangar la'antar haramtacciyar kasar Isra'ila da yin allawadai da zaluncinta da take yi kan al'ummar palastinu marassa kariya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci a kasar Thailand sun yi wata gagarumar zanga-zangar la'antar haramtacciyar kasar Isra'ila da yin allawadai da zaluncinta da take yi kan al'ummar palastinu marassa kariya da suka kwashe tsawon lokaci suna fuskantar zaluncin wannan haramtacciyar kasa.

Wani rahoton kuma Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya sanar da cewa; haramtacciyar kasar Isra'ila ba zata amince kasar Masar ta jibge sojoji masu yawa a tsibirin Sina mallakin kasar ta Masar ba Isra'ila Ta Hana Kasar Masar Jibge Sojojinta A Tsibirin Sina Na Masar.
Jaridar Ha'aretz a shafinta na Internet ta bayyana cewar a jiya asabar ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila Ihud Barak ya sanar da cewar haramtacciyar kasar Isra'ila ba zata amince da shirin kasar Masar na jibge sojoji masu tarin yawa a tsibirin Sina da ke kusa da kan iyaka da Isra'ila ba.
A gefe guda kuma Mujallar Economist da ake bugawa a kasar Birtaniya a fitowarta ta ranar Juma'a ta bayyana cewa; Ihud Barak ya furta cewar idan gwamnatin Masar zata jibge sojojin masu yawa a tsibirin na Sina da nufin magance tashe tashen hankula da suke faruwa a kan iyakarta da haramtacciyar kasar Isra'ila ce, to babu matsala zata iya jibge sojojin domin hakan zai zame amfani ne ga Isra'ila.

850031
captcha