Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa an bayyana cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar Algeria ta karyata abin da ‘yan tawayen kasar Libya suka fada kan cewa, Gaddafi ya gudu ya shiga cikin kasar tare da wasu daga cikin iyalansa inda suka ce gwamnatin Algeria ta ba shi mafakar siyasa.
Bayanin ya ci gaba da cewa A cikin wannan ayar za mu iya fahimtar cewa Allah madaukakin sarki yana cewa da muminai su ci daga ababe kyawawa da daga arzikin da ya huwace musu, duk da cewa a lokaci guda Allah ba yana kira zuwa bautar ciki ba ne, wato rayuwar muminai ta zama manufarta ita ce cin abubuwa masu dadi daga arzikin Allah ba kawai.
Wadanan ababe na daga arzikin Allah ba shi ne manufa kawai, illa manufar ita ce godiya gare shi bisa ni’imarsa da samun karfin gwiwa wajen ibadarsa, kasantuwar mutum mai bukatuwa ne bisa dabi’arsa ta halitta zuwa ga abin da zai karfafa halittarsa ta jiki wajen yin aiki a cikin rayuwarsa.
Aiki na gari tamkar ‘ya’yan marmari ne a cikin lambu, a lokacin da mutum yake aikata abin da Allah ya umurce shi kuma yake hanuwa daga haninsa, hakan ya fi soyuwa gare shi fiye da kayan marmari na cikin lambu da yake shifkawa da hannunsa, saboda haka dole ne ni’imar ubangiji ta zama hanya ce ta kara yin godiya gare shi daga bayinsa.
851115