IQNA

Babban Malamin Al-Azhar Ya Taya Musulmi Murnar Idil Fitr

12:55 - August 31, 2011
Lambar Labari: 2179753
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami’ar Azhar ya taya dukkanin musulmi murnar idin karamar salla na wannan shekara tare da yin fatan alkhairi ga dukkanin musulmin duniya baki daya da kuma shugabannin kasashen musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-aharam ta kasar Masar an bayyana cewa, malamin jami’ar Azhar ya taya dukkanin musulmi murnar idin karamar salla na wannan shekara tare da yin fatan alkhairi ga dukkanin musulmin duniya baki daya da kuma shugabannin kasashen musulmi na duniya baki daya, tare da rokon Allah ya kawo zaman lafiya ga al’ummar musulmi baki daya.
Ahamd Tayyib ya kirayi dukaknin musulmi da su kokari su dinke duk wata baraka atsaknainsu, Akwai wadansu mutane da suke da'awar cewa Alkur'ani dai ba mu'ujiza ba ne, to idan har abin da suke fadi gaskiya ne, to shi kenan su rubuta wani litttafi da irin wadannan haruffa kamar yadda ya zo cikin Alkur'ani sannan kuma a fagen jumloli ya zamanto maras tamka haka nan kuma a bangaren abubuwan da ya kumsa.
Lalle wannan yana daga cikin fasahar Ubangiji wanda ya samar da wani littafi daga wadannan haruffa da muka saba ganinsu ta yadda dan'adam zai gaza hatta wajen samar da wata sura ko da guda ce, kamar yadda hakan ta faru a duniya ta dabi'a inda Allah Madaukakin Sarki ya ke samar da nau'oi daban-daban na tsirrai da 'ya'yan itatuwa daga wata kasa macacciya maras rai.
852436

captcha