Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaq news an bayyan acewa, ofishin babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyis Ali Sistani ya sanar da ranar laraba a matsayin ita ce ranar idin fitr na wanna shekara a kasar ta Iraki baki daya, tare da yin fatan alkhairi ga dukaknin al’ummar musulmi.
Wannan littafi mai girma wanda wani gado ne na mutanen da suka gabata har zuwa ga mutanen wannan zamanin sannan kuma wanda ya sami damar isar da sakonni da kuma manyan ma'anoni da ilmummuka ga dukkanin bil'adama.
Duk kuwa da cewa ba wai an saukar da Alkur'ani ne daga sama a lokacin guda ban e, to amma sakamakon kariya ta Ubangiji da wannan littafi ya ke da shi ba a sami komai kashin wani sauyi ko gurbata a cikinsa ba. Manzon Allah (s) ya kasance yana karanta wa wasu daga cikin sahabbansa abin da aka saukar masa su kuma suna rubutawa sannan wasu kuma daga cikinsu suna haddacewa.
A lokacin da mutum ya karanci wannan littafi na Ubangiji da kyau, ko shakka babu zai fahimci cewa lalle wannan littafi daga wajen Allah ya ke, don kuwa irin bayanai da masaniyar da ke cikinsa wani lamari ne da ba ma za a yi tunanin ganinsa daga wajen wani mutum, shi din ma mutumin wancan lokaci da ilimi da masaniya suka yi karanci.
Kamar yadda muka fadi a shiri na farko a matsayin gabatarwa mun fadi cewa Alkur'ani littafi ne na shiriya da jan bil'adama zuwa ga sa'ada da farin ciki. Duk wanda ya kasance mai neman sa'ada, to ba shi da wata hanya da ta wuce ya koma ga wannan littafi da Allah Mahalacci ya aiko masa, sannan kuma ya yi amfani da hanyoyi da kayan aiki da ya ke da su wajen nesantar abubuwan da suke barazana ga ruhi da kuma jikinsa.
852330