Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a labarin da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar al'alam cewa, daya daga cikin fitatun 'yan siyasa na kasar Libya Sanusi basikari ya bayyana irin wayewar da ya ce al'ummar Libya na da ita a matsayin wani babban abin da zai hana kasashen yammacin turai hana tabbatar da manufarsu a kasar wadda take da dimbin arzikin manfetur.
A wani rahoton kuma da yake da dangantaka da rikicin na kasar Libya jakadan Libiya a kasar Zimbabwe ya fice daga cikin Zimbabwe bayan da gwamnatin kasar ta kore shi saboda hadewa day a yi da 'yan tawaye da suke dauke da makamai, kuma suke samun goyon bayan kasashen yammacin turai..
Gidan radiyon gwamnatin Zimbabwe a jiya juma'a ya sanar da cewa; Jakadan kasar Libiya a Zimbabwe Tahir Al-Muqrahi ya fice daga cikin kasar Zimbabwe zuwa kasar Botswana ta hanyar mota saboda matsalar rashin jigilar jiragen sama a kasar Zimbabwe sakamakon yajin aiki da ma'aikatan kwamfanonin jaragen sama ke yi a kasar.
A makon da ya gabata ne gwamnatin kasar Zimbabwe ta bada wa'adin wasu kwanaki ga jakadan kasar ta Libiya kan ya fice mata daga cikin kasa bayan da ya bayyana goyon bayansa ga masu bore a Libiya, kuma ya sauke tutar Libiya ya daga na Majalisar Wucin Gadi da ke wakiltan masu bore a kasar ta Libiya a kan ofishin jakadancin Libiya da ke birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe.
853204