IQNA

Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi A Jordan ta Bukaci A Kori Jakadan Isra'ila

16:49 - September 05, 2011
Lambar Labari: 2181879
Bangaren kasa da kasa, kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar Jordan ta bukaci da akori jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila da ke kasar kamar yadda kasar Turkiya ta yi a cikin wannan mako.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-inqaz an bayyana cewa, Ikhwanul muslimin a kasar Jordan ta bukaci da akori jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila da ke kasar kamar yadda kasar Turkiya ta yi a cikin wannan lokaci.
Gwamnatin Turkiya ta bayyana azamarta ta daukar matakan shari'a dangane da matsayin killace yankin Gaza ta fuskar dokokin kasa da kasa, ministan harkokin wajen Turkiya Ahmad Uglu Da'ud ya fadawa tashar telbijin din kasar ta T.t.t cewa a mako mai zuwa ne kasarsa za ta shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa da ta ke birnin Huage akan takunkumin da Isra'ila ta kakabawa yankin Gaza.
A jiya juma'a ne dai gwamnatin Turkiya ta maida martani akan rahoton majalisar dinkin duniya dangane da kashe turkawa 9 da sojojin haramtacciyar Kasar isra'ila su ka yi a 2010 wanda ya ki dora alhaki akan gwamnatin Sahayoniya martanin na Turkiya ya kunshi korar jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila daga birnin Ankara da kuma rage alakar soja tsakanin bangarorin biyu.
Shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa yana daga cikin matakan da turkawan su ka yi alkawalin dauka akan haramtacciyar kasar ta yahudawan sahyuniya, wadda ta zama karfen kafa ga zaman lafiyar duniya.
854308


captcha