Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakkausar suka kan rahoton da aka fitar dangane da harin ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan al'ummar yankin zirin Gaza.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga tashar talabijin din kasar Lebanon ta Al-manar cewa kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakkausar suka kan rahoton da aka fitar dangane da harin ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan al'ummar yankin zirin Gaza inda ta kasha dubban fararen hula.
Cikin shirin da ya gabata, mun yi ishara da cewa daya daga cikin abubuwan da yahudawa su ke sukar musulmi da shi, shi ne batun sauya alkibla daga Baitul Mukaddas zuwa makka. Wannan ayar da kuma ayoyin da su ka zo bayanta suna yin magana ne a fili dangane da wannan batun sannan kuma ta ke maida martani akan hakan.
Bayan aike, manzon Allah ya dauki shekaru goma sha uku a makko ya rika fuskantar Baitul Mukaddas yana yin salla. Domin kuwa albibla ce wacce dukkanin masu bautar Allah su ke girmamawa, wuri ne kuma da dukkanin addinai su ke girmamawa.
855593