IQNA

Shugaban Ofishin Jakadancin Masar Na Tattaunawa Da Isra'ila

20:04 - September 13, 2011
Lambar Labari: 2186835
Bangaren kasa da kasa, shugaban ofishin jakadancin kasar Masar a haramtacciyar kasar Isra'ila tare da wata babbar tawagar yahudawan sahyuniya sun isa birnin masar domin tataunawa kan batun komawar jakadansu a kasar Masar.



Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban ofishin jakadancin kasar Masar a haramtacciyar kasar Isra'ila tare da wata babbar tawagar yahudawan sahyuniya sun isa birnin masar domin tataunawa kan batun komawar jakadansu a kasar, bayan da massu bore suka kore shi a makon jiya.

A wani labarin kuma, fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila zata ci gaba da mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da ke tsakaninta da kasar Masar.

A furucin da ya fito daga bakin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kwana daya bayan harin da jama'ar kasar Masar suka kai kan ofishin jakadancin h.k.Isra'ila da ke birnin Alkahira; Benyamin Netanyahu ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila zata ci gaba da mutunta yaejejeniyar zaman lafiya da ke tsakaninta da kasar Masar domin hakan shi ne masalahar kasashen biyu, kuma gwamnatin h.k.Isra'ila tana ci gaba da tuntubar gwamnatin Masar domin ganin jakadan Isra'ila ya koma kasar ta Masar cikin hanzari.

Netanyahu ya kuma jinjinawa gwamnatin Masar kan matakin da ta dauka na 'yanto jami'an tsaron h.k.Isra'ila shida da aka yi garkuwa da su a cikin ofishin jakadancinta da ke kasar ta Masar, kamar yadda ya yaba wa shugaban kasar Amurka Barak Obama kan tsoma bakin da ya yi na ganin gwamnatin Masar ta hanzarta daukan matakin shawo kan masu zanga zangar da suka killace ofishin jakadancin h.kasar ta Isra'ila da ke Masar.
859342
captcha