IQNA

Kiristocin Na Mara Baya Ga Musulmi A Boren Kasashen Larabawa

13:32 - September 14, 2011
Lambar Labari: 2187316
Bangaren kasa da kasa, wata malamar jami'a daga kasar Lebanon ta bayyan acewa mabiya addinin kirista suna mara baya ga musulmi wajen shiga cikin yunkurinsu da nufin ganin adalci ya samu wurin zama acikin kasashensu.



Kmafanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoton da ke cewa wata malamar jami'a daga kasar Lebanon ta bayyan acewa mabiya addinin kirista suna mara baya ga musulmi wajen shiga cikin yunkurinsu da nufin ganin adalci ya samu wurin zama a cikin kasashensu musamman a cikin 'yan wattannin farkon shekarar nan ta bana.

A bangare guda kuma Kungiyar kasa da kasa mai kare hakkokin kananan yara da fada-fadan coci suka yi lalata da su ta bukaci kotun kasa da kasa mai hukumta manyan laifufffuka da ta gurfanar da Paparoma Benedict na 16 a gabanta da zargin laifin cin zarafin bil'adama.
Ita dai wannan kungiya mai suna wacce take birnin hicago na kasar Amurka ta ce ta shigar da kara zuwa ga kotun kasa da kasar inda ta bukaci kotun da gurfanar da Paparoman da wasu manyan jami'an fadar Vatican su uku saboda hannun da suke da shi cikin laiffuffukan cin zarafin bil'adama da suka hada da fyade da sauran ayyuka na lalata a duk fadin duniya.
A cikin wata sanarwa da lauyoyin kungiyar suka fitar sun bayyana cewar manyan jami'an fadar Vatican din suna sane da cin zarafi da lalata da dubun dubatan mutane mafiya yawansu kananan yara da malaman coci suke yi amma kuma sun rufe lamarin. Har ila yau lauyoyi sun aike wa kotun wasu bayanai cikin sama da shafuka da suke nuni da irin danyen aikin da malaman kiristan suka yi tsawon shekaru.
860585


captcha