Bangaren kasa da kasa, daliban jami’a a kasar Masar sun gudanar da wani gangami a birnin Alkahira inda suka banka wa tutar kasar Amurka wuta suka kone ta kurmus, kuma sun yi gangamin ne a gaban jami’ar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi ta kasdar Masar cewa daruruwan daliban jami’a a kasar Masar sun gudanar da wani gangami a birnin Alkahira inda suka banka wa tutar kasar Amurka wuta suka kone ta kurmus, kuma sun yi gangamin ne a gaban jami’ar Amurka da ke cikin birnin na Alkhira.
A cikin taken da suka yi ta rerawa alokacin zanga-zangar daliban sun jaddada cewa al’adun Amurka ba su da wurin zama a cikin kasar Masar, saboda haka dole ne ta sanda inda dare ya yi mata tun kafin korewar lokaci.
Makon da ya gabata ne dubban mutanen kasar Masar akasarin matasa masu bore suka kai farmaki kan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke cikin birnin Alkahira, inda suka rushe katangar da mahukuntan kasar suka gina domin kare jamia’n diplomasiyar yahudawan sahyuniya.
Rahoon ya tabbatar da cewa daliban jami’a a kasar Masar sun gudanar da wani gangami a birnin Alkahira inda suka banka wa tutar kasar Amurka wuta suka kone ta kurmus, kuma sun yi gangamin ne a gaban jami’ar Amurka a Masar.
863127