IQNA

Palasdinawa Sun Nuna adawa Da Harin Da Yahudawa Suka Kaiwa Masallacin Kudus

17:49 - September 20, 2011
Lambar Labari: 2190883
Bangaren kasa da kasa;Palasdinwa sun nuna rashin jin dadi da adawa da harin da yahudawa masu tsautsauran ra'ayi da baker nuna gaba da kiyayya suka kai wa masallacin kudus mai tsarki da kuma suka samu taimako da kariyar sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kamfanin dillancin labarai na iknna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Palasdinwa sun nuna rashin jin dadi da adawa da harin da yahudawa masu tsautsauran ra'ayi da baker nuna gaba da kiyayya suka kai wa masallacin kudus mai tsarki da kuma suka samu taimako da kariyar sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila.yahudawa yan share guri zauna da kuma masu tsananin adawa da gaba da musulmi sun shere shekaru da shekaru na gallazawa Palasdinawa da kuma kai wa wannnan masallaci mai alfarma na kudus hari kuma suna samin goyan baya da kariya daga sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da gwamnatin Haramtacciyar kasar ta isra'ila da siyasarta ta shinfido da ginuwa kan zalunci da danniya a yankin da duniya baki daya.


863714

captcha