IQNA

Shugaban Kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ya Koma Kasar Bayan Jinya

15:45 - September 24, 2011
Lambar Labari: 2192374
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Yemen Ali Abdllah saleh ya koma kasar bayan kwashe tsawon watani uku yan ajinya a kasar Saudiyya biyo bayan harin da aka kai kansa a fadarsa da ke birnin Sana’a.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reauters cewa, Abdallah saleh na kasar Yemen ya koma kasar jiya bayan kwashe tsawon watani uku yan ajinya a kasar Saudiyya biyo bayan harin da aka kai kansa a fadarsa da ke birnin Sana’a a cikin watannin da suka gabata.
Saleh ya kwashe tsawon watanni uku ne cur a kasar Saudiyya ana kula da shi tare da yi masa maganai, bayan samun sauki ya aike da sako ta hanayar hoton talabijin ga magoya bayansa na kasar Yemen cewa yana nan dawowa da zaran ya kam akarbar magani,kuma zai bayar da dama a gudanar da zabuka.
Kasar Sudiyya dai ce ta ba shi mafaka kuma take taimaka masa da makamai da kudi domin ya murkushe masu neman sauyi ta hanyar lumana a kasar, wanda dullanin kungiyoyin kare dan adam na kasar suka yi Allawadai da matakin na Saudiyya.
Yanzu haka dai Saleh yana ci gaba da kasseh mutane bayan dawowartasa ba ta wuce ‘yan sa’oi ba, lamarin da yake kara dora alamar tambaya dangane da abin suka shirya shi da mahukuntan Saudiyya kan murkushe masu neman sauyi.
866165


captcha