IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Yi Allawadai Da Kashe Rabbani

15:44 - September 24, 2011
Lambar Labari: 2192375
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta kakkausar suka da yin Allawadai da kashe tsohon shugaban kasar Afghanistan Burhanuddini Rabbani wanda aka kai harin kunan bakin wake kansa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na jaridar Al-intiqad cewa, kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta kakkausar suka da yin Allawadai da kashe tsohon shugaban kasar Afghanistan Burhanuddini Rabbani wanda aka kai harin kunan bakin wake kansa a gidansa da ke birnin Kabul.
Kungiyar ta ce hakan yana misilta hakinanin aikin ta’addanci ne kan mutanen da suke neman sulhu da zaman lafiya acikin al’umma,kuma duk wanda suke da hannu wajen shirya kai wannan hari na ta’addanci ba su son zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar ta Afghanistan.
Rahoton da kafofin yada labarai suka bayar ya yi nuni da cewa taron janazar ya samu halartar dubban mutane da suka hada da manyan jami’an gwamnatin afghanistan da suka hada da shugaban kasar Hamid karazai, da kuma wasu manyan baki daga kasashen ketare a cikin tsauraran matakai, an gudanar da janazar a masallaci Ark.
Lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron janazar shugaban kasar Afghanistan Hamid Karazai ya bayyana burhanuddini Rabbani a matsayin wani gwarzo wanda ya yi shada a tafarkin gaskiya da neman sulhu da zaman lafiya atsakanin dukkanin al’ummar musulmi ta kasar Afghanistan.
Ya jaddada cewa zai ci gaba da gudanar ada abin da yake yi na neman sulhu da kungiyar taliban domin kawo karshen zaman zullumi da rashin tabbas a kasar baki daya, wanda hakan ba zai yiwu matukar dai ba a yi sulhu da Taliban ba wadda ita ce kan gaba wajen aiwatar da irin wadannan ayyuka.
866138











captcha