Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya na kalto wani rahoto da ke cewa ministocin kiwon lafiya na kasashen musulmi za su gudanar da zaman taronsu a birnin Astaneh na kasar Qazagistan ranakun Alhamis zuwa Asabar mai zuwa kamar dai yadda babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya fada.
Ikmaluddini Auglo zai gabatar da jawabin bude taron tare da halartar mambobi na kasshe kungiyar 57 da kuma mahalarta akalla 30 na cikin gida da kuma kasashen ketare, inda za su tattauna muhimamn batutuwa da suka danganci matsaloli na kiwon lafiya acikin kasashen musulmi, da kuma irin gudunmawar da ake bukata da bangarorin da ake da bukatar.
Abin takaici ne cewa wasu mabiya addinan da ba su da cikakkiyar masaniya akan koyarwar addini, suna zaton cewa suna da matsayi na musamman a wurin Ubangji, kuma da su kadai ne Ubangiji ya damu, kuma saboda su kadai ne ya aiko annabawa, saboda haka ba a shirye su ke ba su yi imani da wasu annabawa kuma ba su cikin masu yi musu biyayya.
Allah madaukakin sarki ba shi da dangantaka da wata kabila ko da wasu iyalai domin kuwa a wurin kowa da kowa daidai wa daida su ke. Abu guda daya wanda ya ke sa mutane su kusance shi ko su yi nisa da shi shi ne aikin da su ke yi, kuma kowane mutum aiki da ya yi ne yake bibiyyarsa.
867258