Bangaren kasa da kasa, al’ummomin musulmi da na larabawa suna ci gaba da mikewa domin kalubalantar azzaluman shugabanni da sarakuna da suke wasa da hakkokin mutane tare da mika su ga siyasar manyan kasashen duniya masu girman kai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto cewa, babban daraktan radiyon Nur da ke watsa shirye-shiryensa daga birnin Beirut na kasar Lebanon ya bayyana cewa, a halin yanzu al’ummomin musulmi da na larabawa suna ci gaba da mikewa domin kalubalantar azzaluman shugabanni da sarakuna da suke wasa da hakkokin mutane tare da mika su ga siyasar manyan kasashen duniya masu girman kai bayan da suka sayar da mutuncinsu da addininsu domin mulki da duniya.
Ya ci gaba da cewa kafofin yada labarai na kasashen duniya sun kasa nakalto hakikanin abin da yake faruwa a kasar Bahrain an cin zarafin dan adam da keta hurumin addini wanda mahukuntan kasar suke aikatawa tun bayan fara zanga-zangar neman sauyi.
Ya kara da cewa kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun shafe duk wata alama ta musulunci ta hanyar yakin ruwan sanyi da suke yi da musulmi a wasu yankunan, a wasu kumata hanyar yaki da makami domin su mamaye su da arzikinsu da siyasarsu.
868721