IQNA

Gwamnatin Niger Ta Ce Za Ta Bayar Da Dama A Binciki Dan Gaddafi A Kasarta

11:56 - October 03, 2011
Lambar Labari: 2197978
Bangaren kasa da kasa, ministan kula da harkokin shari'a na jamhuriyar Niger ya sheda cewa majalisar rikon kwarya ta kasar Libya za ta iya gudanar da bincike kan maboyar da kanal Gaddafi wanda ya gudu ya shiga cikin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na afriuinfos cewa, Maro Amadou ministan kula da harkokin shari'a na jamhuriyar Niger ya sheda cewa majalisar rikon kwarya ta kasar Libya za ta iya gudanar da bincike kan maboyar da kanal Gaddafi, domin gabatar da shi ga shari'a kamar yadda hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa ta bukaci hakan.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabinsa da gidan talabijin din kasar Niger ya watsa kai tsaye, inda ya bayyana cewa kasarsa ta amince da majalisar wucin gadin kasar Libya a hukumance, saboda haka suna da damar su shigo cikin Niger da 'yanci su kame Sa'idi Gaddafi.

Ya kara da cewa duk wannan damar da suka baiwa majalisar wucin gadin kasar Libya, amma kuma hakan ba ya nufin cewa za su kame shi su mika shi ga sabbin mahukuntan ba ne.

Bayan faduwar gwamnatin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Saidi Gaddafi ya shiga cikin kasar Niger domin neman mafaka, inda ake zaton cewa yanzu haka yana arewacin kasar.

871275




captcha