Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da tofin Allah tsine kan yadda aka cinnawa masallaci wuta a kauyen Duba Zangariya da ke yankin Aljalil na Palasdinu da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye.Ikmalul Din Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a cikin wani bayani day a fitar cikin kaukausar murya ya yi Allah wadai da hari da kuma cinnawa masallacin Jalil Wuta da yahudawa yan sahyoniya masu tsauraren ra'ayi suka yi a wanin halin na zalunci da nuna wuce gonad a iri. Wani wani sabon mataki ne na takalar fada a daidai lokacin da ake kokarin samara da kasar Palasdinu mai cin gashin kanta da kawo karshen wannan takaddama da mamaye na zaluncin Haramtacciyar kasar Isra'ila da masu mara mata baya Amerika da kasashen yammacin turai.
872995