Bangaren kasa da kasa, mutanen kasar Iraki da suka hada da fararen hula da kuma ‘yan siyasa sun fito karara sun nuna rashin amincewarsu da shirin da gwamnatin Iraki take da shi a barin wasu daga cikin sojojin mamayar Amurka da suke cikin kasar domin horar da jami’an tsaro da sojoji.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din al-alam cewa, da dama daga cikin mutanen kasar Iraki da suka hada da fararen hula da kuma ‘yan siyasa sun fito karara sun nuna rashin amincewarsu da shirin da gwamnatin Iraki take da shi a barin wasu daga cikin sojojin mamayar Amurka da suke cikin kasar domin horar da jami’an tsaro da sojoji zuwa karshen wannan shekara da muke ciki ta 2011.
Wannan matasaya dai ta zo bayan da wasu daga cikin ‘yan siyasar kasar Iraki musamman wadanda suke wakltar jama’a a majlaisar dokokin kasar suka amince kan cewa, wasu daga cikin sojojin mamaya da yawansu ba zai wuce dubu biyar ba, za su iya tsayawa domin bayar horo ga sauran sojojin kasar Iraki, amma hakan ya fuskanci fushin al’umma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen kasar Iraki da suka hada da fararen hula da kuma ‘yan siyasa sun fito karara sun nuna rashin amincewarsu da shirin da gwamnatin Iraki take da shi a barin wasu daga cikin sojojin mamayar Amurka da suke cikin kasar domin horar da jami’an tsaro na kasar ta Iraki.
876923