Kamfanin dillancin lbarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; firaministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a hanyar da suka saba ta wuce gonad a iri da gwamnatin ta ke yi a kan hakkokin Palasdinu ya bada labarin kafa wani komitin da zai lalubo hanayr dokantar da matsugunnan yahudawa yan share guri zauna. Yakub Ni'iman ministan shari'a na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila shi ne aka daurawa wannan nauyi na zakulo mambobin komitin da kuma nauyin bin hanyoyi na sharia'a da karyawa inda babu gaba domin tabbatar da wannan mummunar manufa.
878414