Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar mallakin kungiyar Hizbullah an bayyana cewa, mataimakin babban sakataren kungiyar Shekh Na’im Kasim ya bayyana cewa, manufar kirkiro tuhumar Iran kan batun neman yin kisan gilla kan jakadan kasar Saudiyya a kasar ita ce kokarin bata sunan Iran da rage tasirinta a cikin duniya musamman ma kasashen musulmi da na larabawa, bisa la’akari da gagarumar rawar da take takawa wajen fadakar da mutane kan makircin turawa.
A bangare guda kuma jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kuma bayyana cewa: A kullum makiya suna cikin tunanin kulla sharri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne, amma Allah cikin ikonsa yana rusa duk wani makircin da suka kitsa. Jagoran ya kara da cewa: ko a cikin 'yan kwanakin nan kafofin watsa labaran da suke da alaka ta kud da kud da Yahudawan Sahayoniyya sun yi ta yayata zargi maras tushe da gwamnatin Amurka ta yi kan wasu Iraniyawa mazauna Amurka, a kokarin da Amurka ke yi na bata sunan kasar Iran tare da bayyana ta a matsayin kasar da ke kare ayyukan ta'addanci a duniya, amma wannan makirci babu wani tasirin da zai yi.
A cikin 'yan kwanakin nan ne dai gwamnatin Amurka ta hanyar kafofin watsa labaran da suke karkashin tasirin siyasarta suka dinga yada zargi maras tushe kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran na cewa wai tana shirya makarkashiyar aiwatar da kisan gilla kan jakadan Saudiyya da ke kasar Amurka, kuma har an kame wani ba'amerike dan asalin kasar Iran kan zargin, lamarin da ya bai wa gidan sarautar Ali-Sa'ud damar shelanta Iran a matsayin kasa mai hatsari a yankin gabas ta tsakiya.
Gwamnatin Amurka ta yi kokarin ganin ta hanyar wannan zargi maras tushe ta cimma bakar siyasarta kan kasar Iran, inda daga gabatar da zargi kan wasu mutane biyu kacal har ta fara batun daukan matakin kakaba ma kasar Iran takunkumi mafi muni da kokarin mai da ita saniyar ware a duniya. To sai dai wannan zargi na makirci ko a tsakanin jami'an Amurka bai samu karbuwa ba, inda masana harkar siyasa da na tsaro a cikin Amurka suka bayyana zargin a matsayin wasan yara da ba a zufafa tunani ba wajen gabatar da shi.
A karshe jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana kokarin da gwamnatin Amurka ke yi neman bata sunan kasar Iran a idon duniya da cewa; wani bangare ne na makirce -makircen da kasashe masu girman kai na duniya ke kitsawa da nufin cimma bakar siyasarsu ta zalunci, to sai dai masu magana na cewa; munafuncin dodo ya kan ci mai shi, musamman idan aka yi la'akari da yadda kasar Amurka ta zame ita ce abin kyama a tsakanin al'ummomin duniya, baya ga matsalolinta na cikin gida musamman yunkurin baya bayan nan na Wall-Street na fada da babakeren 'yan jari hujja.
880496