IQNA

Adadin Mutanen da Suka Rasa Rayukansu A Daren Jiya Ya Kai Takwas

14:09 - October 18, 2011
Lambar Labari: 2207285
Bangaren kasa da kasa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ake gudanarwa a kasar Yemen a daren ranar lahadi da ta gabata domin neman shugaba Saleh ya yi murabus sun kai mutane tkwas akalla.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran AFP na kasar Faransa cewa, rahotannin sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ake gudanarwa a kasar Yemen a daren ranar lahadi da ta gabata domin neman shugaba Ali Abdallah Saleh ya yi murabus sun kai mutane tkwas tare da jikkatar wasu da dama, wadanda su ma adadinsu ya kai mutum sattin.
Bayanin ya ci gaba da cewa dubban daruruwan mutanen da suka gudanar da zanga-zangar neman shugaba Saeh da ya safka sun hadu da dabbancin jami’an tsaronsa, wadanda suke samun goyon baya na kasar saudiyya da Amurka, inda suka yi ta harbinsu da harsasai masu rai, tare da kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu.
A cikin rahoton da aka bayar an nuna cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ake gudanarwa a kasar Yemen a daren ranar lahadi da ta gabata domin neman shugaba Saleh ya yi murabus sun kai mutane tkwas akalla yayin da wasu gomin na daban suka samu munan raunuka.
881532


captcha