IQNA

Masu Juyin A Kasar Libiya Sun Yantar Da Bani Walid

15:14 - October 19, 2011
Lambar Labari: 2208154
Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin komandodin masu juyin juya hali a kasar Libiya ya bada labarin Yantar da garin Bani Walid daga hannun dakarun da ke biyayya ga Mu'ammar Kadafi.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa : : Daya daga cikin komandodin masu juyin juya hali a kasar Libiya ya bada labarin Yantar da garin Bani Walid daga hannun dakarun da ke biyayya ga Mu'ammar Kadafi.Saif Allasi daya daga cikin jagororin dakarun masu juyin a kasar Libiya a wata tattaunawa da gidan talbijin na Al'alam da ke watsa shirye-shiryensa ta hanyar tauraron dan adam daga nan birnin Tehran ya bayyana cewa; a ranar ashirin da biyar ga watan Mehr na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne suka kakkabe wannan gari na Bani Walid da dakarun da ke yin biyayya ga Muammar kaddafi hambararr shugaban kasar Libiya. Ya ci gaba da cewa yanzu za su nufi gabacin kasar zuwa birnin Sirt .


882035
captcha