IQNA

Mummunan Karshe Ga Mai Zubar Da Jinin Al’umma Ya Tabbatar Da Alkawalin Allah

15:09 - October 22, 2011
Lambar Labari: 2209451
Bangaren kasa da kasa, sarkin sarakunan dukkanin nahiyar Afirka, jagoran sarakuna da shugabannin larabawa, jagoran jamhuriyar larabci ta Libya na daga cikin kalmomin da larabawa ba za su kara jinsu daga tsohon jagoran Libya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan mutuwar tsohon shugaban mulkin kama karya Gaddafi, wannan take na sarkin sarakunan dukkanin nahiyar Afirka, jagoran sarakuna da shugabannin larabawa, jagoran jamhuriyar larabci ta Libya na daga cikin kalmomin da larabawa ba za su kara jinsu daga gare shi ba bayan da ya hadu da gamunsa ahannu ‘yan tawaye suka rutsa da shi a mahaifarsa.
Wasu majiyoyin hukumar wucin gadin kasar sun habarta cewa wani mayaki ne ya kashe shi bayan an kama shi da ransa amma yana da raunuka sakamakon farmakin da mayakan hukumar suka kai a maboyarsa. Wasu majiyoyin kasashen Yammaci kuwa cewa suka yi an kashe gaddafi ne a wani harin jiragen sama da mayakan kuyngiyar NATO suka kai kan ayarin motocin da gaddafi yake cikinsu a kan hanyarsa ta ficewa daga garin Sirte. Sai tabbatatun labarai suna nuna cewa mayakan juyi ne suka kashe Gaddafi ba sojin NATO ba.

Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi OIC kuwa ta yi wa alummar kasar Libya barka da kawo karshen Gaddafi tare da kuma yin kira ga jamaar kasar da su hada kai domin gina sabuwar kasar Libya. A cikin sanarwar da ya fitar a daren jiya, babban sakataren kungiyar Akmaluddin Ihsan Oglu ya bukaci yan Libyan su tabbatar da hadin kai na bangarorin kasar baki daya sannan kuma su mara baya wa hukumar wucin gadin kasar.

Shi kuma sakataren janar na kungiyar kasashen Larabawa Nabil al-Arabi ya bukaci mutanen Libya su mance da rikice-rikicen da suka faru a baya su samar da hadin kai da sasantawa tsakanin bangarorin kasar domin su sami damar daura damarar gina makomar Libya.

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban KiMoon ya ce kashe Muammar Gaddafi ya bude wani sabon shafi a tarihin kasar Libya amma da akwai sauran aiki a gaban mutanen Libya kafin su cimma manufarsu ta kafa mulkin demokiradiya. Ban KiMoon ya karta da dewa dukkan yan kasar Libya su bada gudummowarsu domin tabbatar da cewa hukumar wucin gadi ta sami nasarar gudanar da zabuka a kasar.
883967
captcha