Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Mahmud Jibril shugaban komitin zartarwa na komitin wadanda suka gudanar da juyi a kasar Libiya da hambarar da gwamnatin Mu'ammar Kaddafi daga kan karagar mulki da kuma kasha shi sun bukaci gwamnatin kasar Aljeriya da ta mika mata iyalan Mu'ammar Kaddafi .Jibril ya kara da cewa ganin masu bore a kasar ne suka kasha Kaddafi da kuma hambarar da gwamnatinsa ya zama dole a mikawa komitin da maido da iyalan kaddafin zuwa kasar Libiya .ya zuwa yanzu ndai matarsa da yayansa biyu da diyarsa shi kaddafi ke gudun hijira a kasar ta Aljeriya tun bayan da birnin Trablus ya fada a hannun masu bore yayinda daya daga cikin yayansa yak e yin gudun hijira a kasar Niger da kuma ci gaba da zama a kasar duk da firijar a mika sag a sabbin mahukumtan na Libiya.
884201