IQNA

An Rufe Batun Hukunta Gaddafi A Kotun Lebanon Kan Batun Imam Musa Sadr

16:00 - October 23, 2011
Lambar Labari: 2210261
Bangaren kasa da kasa, an rufe fayil din hukunta tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya kanar Mu'ammar gaddafi bayan kashe shi a hannun 'yan tawayen kasar a cikin makon nan.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lenbanon files cewa, bangaren shari'a na kasar Lebanon ya rufe fayil din hukunta tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya kanar Mu'ammar gaddafi bayan kashe shi a hannun 'yan tawayen kasar a cikin makon nan a garin Sirt.

A bangare guda kuma shugaban hadakar jam'iyun adawa a kasar Mauritania Mahfuz Wuld Butah ya bayyana matukar farin cikinsa da kashe tsohon jagoran kasar Libya mu'ammar Gaddafi.

Wuld Butah ya bayyana hakan ne a daren jiya a lokacin da yake zantawa da wasu manema labarai a birnin Nuwakshot fadar mulkin kasar Mauritania, inda ya sheda cewa al'ummar kasar Libya sun fama da mulkin kama karya na Gaddafi, wanda ya haramta musu mulki na demokradiyya.

Har yanzu dai gwamnatin Mauritania ba ta amince da majlisar wucin gadin kasar Libya ba, kamar yadda kuma ba ta ce uffan kan kashe kanar Gaddafi ba.

Yanzu haka dai kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun fara yin kiraye-kiraye, na a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar Kanar Gaddafi bayan an kama shi da ransa.

Shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar dinkin duniya ya ce idan kashe Gaddafi aka yi bayan an kama shi da ransa, to hakan na tattare da babban hadari bisa dokoki na kasa da kasa. 884543
captcha