Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; komitin musulunci a Suise IZRS ya bayyana cewa a shirye yake ya biya dukan illahirin kudaden da ake bukata na daukan lauyar da zai kare hakkokin musulmi a gaban kotu da ake kollonsu a matsayin tsuraru.Jaridar Sonntagszeitung da ke fitowa a kasar ta Shis ta nakalto Nicolaus Blancho shugaban komitin musulmin kasar ta Sui IZRS a wata tattauanawa da jaridar na cewa: dukan illahirin musulmin kasar ana muzguna masu da zarar sun bayyana wani abu da ke nuna cewa su musulmi ne da kuma kaskantar da su saboda haka wannan komiti na musulmi ya dau niyar fadada lauyoyi da masu bashi shawara da daukan matakan kare hakkokin musulmi a wannan kasar da kuma kwato masu yancinsu a gaban kotu don haka komitinsu ya dau nauyin biyar dukan kudaden da ake bukata ahr sai sun cimma nasara .
886712