IQNA

Masu kare Hakkin Dan Adam Sun Bukaci Sabon Yariman Saudiyya Da Ya Saki Fursunoni

15:50 - October 30, 2011
Lambar Labari: 2214517
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masu kare hakkokin bil adama da ma marubuta na kasar Saudiyya sun kirayi sabon yarima mai jiran gado a kasar da ya saki fursunonin siyasa da ake tsare da su ba tare da wani laifi ko tuhuma ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin saddarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, masu kare hakkokin bil adama da ma marubuta na kasar Saudiyya sun kirayi sabon yarima mai jiran gado a kasar da ya saki fursunonin siyasa da ake tsare da su ba tare da wani laifi ko tuhuma ba illa dai kawai suna bayyana mahangarsu ta siyasa a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun kafin wannan lokacin mahukuntan kasar Saudiyya suna daukar matakai na rashin imani da rashin tausayi kan masu kare hakkokin bil adama da ‘yan siyasa na kasar, domin kawai suna bayyana mahangarsu kan lamurran siyasa da mulukiya akasar Saudiyya.
Yanzu haka dai masu kare hakkokin bil adama da ma marubuta na kasar Saudiyya sun kirayi sabon yarima mai jiran gado a kasar da ya saki fursunonin siyasa da ake tsare da su ba tare da wani laifi ko tuhuma ba saboda kawai suna adawa da tsarin mulukiya dake tafiyar da kasar.
889194



captcha