IQNA

Mai Bada Fatawa Na Saudiyya Bai Amince Da Kame Sojojin Yahudawan sahyuniya Ba

19:41 - November 03, 2011
Lambar Labari: 2216968
Bangaren kasa da kasa, wani mai bayar da fatawa ga gwamnatin wahabaiyawan Saudiyya ya fito karara ya bayyana rashin halascin kame sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila domin yin garkuwa da su tare da bayyana hakan da cewa ya sabawa sharia’a a mahangarsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na ayanr gizo na jaridar sabaq ta Saudiyya cewa, Abdulmuhsin Ubaikan wani mai bayar da fatawa ga gwamnatin wahabaiyawan Saudiyya ya fito karara ya bayyana rashin halascin kame sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila domin yin garkuwa da su tare da bayyana hakan da cewa ya sabawa sharia’a a mahangarsa da kuma yadda shi yake kallon shari’a a tafarkin wahabiyanci.
A wani mataki da ya yi hannaun riga da wannan an ware makudan kudade da suka kimanin dalar Amurka dubu dari daya ga duk wanda ya kama wani sojan Isra’ila domin yin garkuwa da shi, ta yadda hakan zai taimaka wajen sakin fursunonin larbawa musamman dubbaban palastinawan da suke tsare da su.
Daya daga cikin malaman kasar Sausiyya ne ya sanar da hakan, inda ya ce shi da kansa ne ya dauki alhakin bayar da wannan lada ga duk wanda ya kame sojan Isra’ila tare yin garkuwa da shi, hakan ya zo ne domin mayar da martani kan izgilin da wasu yahudawa suke yi na cewa duk wanda ya sake kama daya daga cikin mutanen da aka saka to za su ab shi lada ta dakla dubu dari.
Ya ce dai ya ware makudan kudade da suka kimanin dalar Amurka dubu dari daya ga duk wanda ya kama wani sojan Isra’ila domin yin garkuwa da shi, ta yadda hakan zai taimaka wajen sakin fursunonin larbawa da palastinawa da suke kurkukun yahudawa daban-daban.
891833


captcha