IQNA

Hassan Saffar Ya Kirayi mahajjata Da Su Karfafa Hadin kai Na Musulunci

16:07 - November 09, 2011
Lambar Labari: 2219972
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin malman addinin muslunci kuma mabiya tafarki iyalan gidan manzon Allah da ke kasar saudiyya sheikh Hassan saffar ya kirayi dukkanin mahajjata zuwa karfafa hadin kai na musulunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya naklato daga safin sadarwa na yanar gizo na tashar RASID cewa, a ci gaba da kokarin wayar da kan musulmi da malamai suke yi daya daga cikin malman addinin muslunci kuma mabiya tafarki iyalan gidan manzon Allah da ke kasar saudiyya sheikh Hassan saffar ya kirayi dukkanin mahajjata zuwa karfafa hadin kai na musulunci domin fuskantar barazanar da ke gaban musulmi.
Malamin ya yi ishara da cewa babu abin da muuslmi za su iya aiwatar na ci gaba matukar kawunansu na rarrabe, domin kuwa musulunci akoda yaushe yana son ganin mabiyansa sun hadu kan manufa daya, kuma wannan wajibi a cikin acikin addinin muslunci, domin kuwa Allah madaukakin sarki ne ya yi wannan umurni.
Daya daga cikin malman addinin muslunci kuma mabiya tafarki iyalan gidan manzon Allah da ke kasar saudiyya sheikh Hassan saffar ya kirayi dukkanin mahajjata zuwa karfafa hadin kai na musulunci, da nufin ganin muuslmi sun zama tsinya daya madaurinki daya.
894762
captcha