IQNA

Abin Da Masu Son Juyi A Bahrain Ba Shi Da Alaka Da Bambanci

16:46 - November 19, 2011
Lambar Labari: 2224809
Bangaren kasa da kasa; Sheikh Ali Sulman babban sakataren jam'iyar Islami Alwifak a kasar Bahrain ya jaddada da cewa: bukatun al'ummar kasar Bahrain masu son kawo sauyi a cikin kasar ko kusa ba shi da alaka da wata kabila ko wata mazhaba b awata ba wata bukata ce ta al'ummar kasar baki daya batare da la'akari da kabila ko akida ba face kawo karshen zalunci da danniya a fadin kasar da kuma kafa mulki na adalci.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa cewa: Sheikh Ali Sulman babban sakataren jam'iyar Islami Alwifak a kasar Bahrain ya jaddada da cewa: bukatun al'ummar kasar Bahrain masu son kawo sauyi a cikin kasar ko kusa ba shi da alaka da wata kabila ko wata mazhaba b awata ba wata bukata ce ta al'ummar kasar baki daya batare da la'akari da kabila ko akida ba face kawo karshen zalunci da danniya a fadin kasar da kuma kafa mulki na adalci.Sheikh Ali Salman yayi wannan furuci ne a daidai lokacin da al'ummar kasar ke gudanar da wata gagaramar zanga zangar kawo karshen mulkin zalunci da danniya a kasar da suka gudanar a jiya juma'a bayan kammala sallar juma'a a fadin kasar ta Bahrain.

900121
captcha