Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa cewa: wata mu'assisar kula da harkokin addini a birnin Kudus ta gano wani gagaramin makircin da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra;ila ke kulla da kitsawa Plasdinawa na gina matsugunnan yahudawa yan share guri zauna. A ranar ashirin da shidda ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a cikin wani bayani da wannan kungiya ta fitar ta bayyana da fallasa wannan babban makirci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kitsawa na mamaye birnin kudus da kuma masallacin Kudus mai girma kumsa kawo fasalin canja salon ginaginai a birnin ya canja daga kamannunsa na tarihi da na musulunci ko kasancewarsa na larabawa da kuma canaja hatta sunayen gurare da ke kewaye da masallacin.
900109