Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-riyad cewa, za a gudanar da wani zaman taro dangae da yadda ake samun karuwar kyamar musulmi da nuna musu banbanci a kasar Amurka wanda zai gudana a birnin Washington fadar mulkin kasar ta Amurka.
A wani labarin kuma an bayyana cewa, wani dan majalisar dattawan Amurka ya bayyana wata doka wacce majalisar zata tattauna a kanta cikin yan kwanakin nan dangane da kasar Iran a matsayin wanda zai durkusadda babban bankin JMI.
Kamfanin dillancin labarai na Al-alam ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a kan shafinsa na Internet, kuma ya kara da cewa, Mik Mic Onil shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawar kasar Amurka dan jam'iyyar Repulican, ya yi Karin bayani bisa wannan dokar, inda y ace, idan an tabbatar da ita, kasar Amurka bata bukatar takunkumin tattalin arziki, ko kuma harin soje kan kasar Iran don kawo karshen shirin tan a makamashin nuklia.
Dokar wacce Mark Kark na hannun damar shugaba Obama daga jam'iyyar ta Republican ya gabatar, zata bawa shugaban damar haramtawa duk wata cibiyar kudi a duniya, ma'amala da harkar tattalin arzikin kasar Amurka, matukar bata kauracewa ma'amala da babban bankin kasar Iran ba.
Kafin nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran dai, shekaru 32 da suka gabata, kasar Iran karkashin Sarki Sha tana daga cikin kasashen gabas ta tsakiya da suka fi zaba jari a cikin cibiyoyin kudade na kasar Amurka.
900194