Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad ta kasar Lebanon cewa, a jiya dubabn daruruwan mutanen kasar Syria sun yi Allawadai da kungiyar kasashen larabawa dangane da matakin da ta dauka na na fitar da kasarsu daga cikin mambobin kungiyar sakamakon matsin lamabar Amurka da ‘yan korenta musamman ma daga cikin kasashen larabawan yankin tekun fasha.
Har yanzu kungiyar hadin kan kasashen larabawa na ci gaba da taka muguwar rawa a rikicin da kasar Syria ta ke fama da shi. Wannan ne ya sa manazarta akan harkokin Siyasa su ke bayyana cewa, akalar kungiyar ta hadin kan kasashen larabawa tana a hannun azzaluman manyan kasashe ne.
A lokacin taron da kungiyar ta yi a Ribat na kasar Moroko a ranar larabar da ta gabata sun baiwa gwamnatin Syria wa'adin kwanaki uku da ta kawo karshen abinda su ka kira: "Zubar da jinin" masu zanga-zanga sannan kuma ta kyale masu sanya ido su shiga cikin kasar.
Ministan harkokin Wajen kasar Katar Sheikh Hamad Bin Jasim Ali Sani, ya fada a wurin taron cewa: Idan daga nan zuwa kwanaki uku Syria ba ta bada hadin kai ba za ta fuskanci takunkumi. Yadda ya yi magana da kakkausar murya yana nuni da cewa an karaci kawo karshen amfani da hanyoyin diplomasiyya wajen yin hulda da kasar Syria.
Wani abu mai jan hankali dangane da taron kungiyar hadin kan kasashen larabawan a moroko shi ne yadda su ke riya cewa suna adawa da tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan Syria, sai dai yadda su ka yi amfani da kakkausan harshe a bayanin bayan taro a kan Syrian, yana nuni da cewa su kansu suna aiwatar da siyasar kasashen waje ne. Suna dakon siyasar kasashen yammacin turai ne ta barna da ta'asa a yankin gabas ta tsakiya.
900590