Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabi9jin din rasid cewa, a jiya jamia’n tsaron masarautar wahabiyawan Saudiyya sun kashe wani matashi a lokacin da ake gudanr da janazar wani matashin da suka kashe a yankin Katif da ke gabacin kasar a cikin lardin Awamiyya wanda akasarin mazaunasa mabiya tafarkin mazhabar iyalan gidan mnzon Allah ne.
A kasar Bahrain kuwa, hadin gwiwar 'yan adawa, 'yan Shi'a na kasar Bahrein, Al-Wefaq, sun fallasa tsararen cin zarafin bil Adama da gidan sarautar kasar ya yi tanadi ga masu zanga-zangar kawo demokarasiya a kasar. A nasu bangare, kungiyoyi ukku na kare hakkin dan Adam na kusa da 'yan adawa, sun wallafa wani rahoto game da yanda gwamnati ke murkushe boren jama'a a cikin kasar a jajiberen kin bayyana rahoton binciken wani komiti mai zaman kansa.
Murkushen boren na jama'ar Bahrein da aka faro tun a watan Fevrier, na gudana ne a wani tsararren shiri, da gidan sarautar ya shirya, inji Wefaq, suka ci gaba da cewa, Tsananin cin zarafin bil Adama ya fuce iyaka, dubunan mutane sun fuskanci nau'in azabatarwa kusan 40. Suna cewa, masu iko sune ke da laifi a game da wannan lamari, suna nuna cewa, sama da mutum 40 suka mutu, an tsare dubunan masu zanga-zanga, an azabatar da dubunne, an kori sama da dalibai 3000 daga makatrantu.
902975