Bangaren kasa da kasa: kungiyoyin siyasa day an takara a neman shugabancin kasar masa a jiya biyu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijra shamsiya sun gudanar da wani taro na binciken abin day a biyo bayan zanga-zangar da matasan kasar suka gudanar a dandalin Tahriri da ke tsakiyar birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta masar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kungiyoyin siyasa day an takara a neman shugabancin kasar masa a jiya biyu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijra shamsiya sun gudanar da wani taro na binciken abin day a biyo bayan zanga-zangar da matasan kasar suka gudanar a dandalin Tahriri da ke tsakiyar birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta masar. Wannan zanga zanga karo na biyu a kasar ta masar musamman a wannan dandali na Tahriri a daidai lokacin da a ke gaf da gudanar da zaban yan majalisar dokoki a kasar wani babban kalubale ne ga mahukumtan kasar da kuma ke tada hankalin yan siyasa day an takara duk da cewa a dabra da haka matasan suna ganin ana son yi masu sakiyar da babu ruwa da maida hannun agogo baya kan gwagwarmayar da suka yin a korar gwamnati da tsohon shugaban kasar Husni Mubarak.
903706