IQNA

Shugaban Kasar Yeman Ali Abdallah saleh Ya Amince Da Sahawar Larabawa

14:58 - November 24, 2011
Lambar Labari: 2228163
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Yeman Ali Abdallah Saleh ya nufi birnin Riyad na kasar Saudiyya domin sanya hannu kan yarjejeniyar mika ragamar mulki ga mataimakinsa wadda za ta fara aiki nan da watanni uku masu zuwa.
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin ta Aljazeera cewa, shugaban kasar Yeman Ali Abdallah Saleh ya nufi birnin Riyad na kasar Saudiyya domin sanya hannu kan yarjejeniyar mika ragamar mulki ga mataimakinsa wadda za ta fara aiki nan da watanni uku masu zuwa kamar dai yadda aka sanar.
Dazu a kasar Saudiyya, shugaban Kasar Yamen Ali Abdallah Saleh da kuma jam'iyyun hamayyar siyasa sun rattaba hannu akan shawarwarin da kungiyar kasashen larabawan yankin tekun pahsa ta gabatar.
Rahotanni da su ke fitowa daga binin Riyadh na kasar Saudiyya sun ce: Ali Abdallah Saleh da kuma gamayyar jam'iyyun hamayyar siyasa na Liqa'ul-Mushtarak, sun sa hannu akan yarjejniyar acikin fadar sarki Abdallah Bin Abdul-Aziz.

"Yarjejniyar ta kunshi mika madafun iko da Ali Abdallah Saleh zai yi ga mataimakinsa Abdu Rabbuh Mansur Hadi, Sai dai samarin da su ke akan titunan San'aa da sauran biranen kasar sun yi watsi da rattaba hannu akan yarjejeniyar wacce su ka kira kokari ne na bada kariya ga shugaba da ya kamata ya gurfana a gaban kuliya saboda kashe mutane da ya yi.
903842


captcha