Bangaren kasa da kasa, an samu wani matashi dan kasar Saudiyya a cikin ‘yan ta’addan kasar Syria da suke kaddamar hari a kan jami’an tsaro da kuma fararen hula a sassan kasar, wanda aka kashe a birin Homs da yake fama tashin hankali da kasashen larabawa da na turai suke haddasawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, an samu wani matashi dan kasar Saudiyya a cikin ‘yan ta’addan kasar Syria da suke kaddamar hari a kan jami’an tsaro da kuma fararen hula a sassan kasar, wanda aka kashe a birin Homs da yake fama tashin hankali da kasashen larabawa da na turai suke haddasawa ta hanayar bayar da makamai ga ‘yan ta’addan.
A nata bangaren gwmanatin kasar Sin ta ce irin matakan da Majalisar dinkin duniya ke dauka dan fuskantar rikcin siyasar kasar Syria, ba abin da za su haifar face mayar da hannun agogo baya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Liu Weimin wanda yake mayar da martani dangane da wani rahoto da Hukumar kare hakkokin bil'adama ta MDD ta fitar kan kasar ta Syria, ya ce tattaunawa ce kawai za ta kai ga warware rikicin da ake fama da shi a kasar a maimaikon yin amfani da hanyoyi na tursasawa.
A cikin daren da ya gabata ne dai hukumar ta kare hakkokin bil'adama ta MDD ta amince da wani kuduri da ke yin tir da kuma Allah wadai da gwamnatin kasar shugaban Basharul Assad, bisa zargin cewa tana cin zarafin bil'adama, kuma yanzu haka kasashen Turai da Amurka na kokarin gabatar wa Majalisa dinkin duniya da wani daftarin kuduri da zai nemi a kakaba wa Syriyar takunkumi ko kuma daukar wasu tsauraran matakai a kanta.
903818