Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; jam'iyar musulunci Wifak milli a kasar Bahrain ta fitar da wata sanarwa da ta kumshi bayanin cewa ta yin Allah wadai da sake cin mutumcin wasu masallatai da gwamnatin Ali Khalfa ta yi da ruguza wasu masallatan.Gwamnatin Baharain ta yi fice a yan watannin nan wajan cin fuska da muzgunawa yan kasar da ke kokowar kawo canji ta fuskar siyasa da ragamar mulkin kasar hatta da kai wa wasu masallatai da guraren ibada hari da ruguza su da hakan ke bayani karara kan bakar siyasar gwamnatin Bahrain.
908313