Bangaren kasa da kasa, a ranar talata mai zuwa ce za a gudanar da taron Ashura a birnin Helesnuki fadar mulkin kasar Filland tare da halartar musulmi daga sassa daban-daban a cikin birnin taron da cibiyar musulunci ta iyalan gidan manzon Allah ta dauki nayuyin shirayawa da gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sautul Iraq cewa, idan Allah ya kai mu ranar talata mai zuwa ce za a gudanar da taron Ashura a birnin Helesnuki fadar mulkin kasar Filland tare da halartar musulmi daga sassa daban-daban a cikin birnin taron da cibiyar musulunci ta iyalan gidan manzon Allah ta dauki nayuyin shirayawa da gudanarwa kamar daii yadda aka saba yi a kowace shekara.
Muhimamn abubuwan da za a yi gudanar wajen taron dai sun hada da karanta wakoki da suka danganci ranar Ashura da shahadar Imam Hussain (AS) da iyalan gidan manzon Allah da aka yi ma yankan rago a karaba, da kuma irin mawuyacin halin da aka saka iyalansa wadanda su ne zuriyar manzon Allah, an kunci da cin fuska.
Daga bisani kuma malamai za su gabatar da jawabi da ya danganci wannan rana, da kuma bayani kan matsayinta a addini da kuma yadda ta kasance mai girma a wajen iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin su tabbata a gare shi alayensa tsarkaka.
A ranar talata mai zuwa ce za a gudanar da taron Ashura a birnin Helesnuki fadar mulkin kasar Filland tare da halartar musulmi daga sassa daban-daban a cikin birnin taron da cibiyar musulunci ta iyalan gidan manzon Allah ta dauki nayuyin shirayawa da gudanarwa shekarun baya.
910008