IQNA

An Yi Allawadai Da Mahukuntan Bahrain Saboda Kai Hari A Kan Tarukan Ashura

17:28 - December 05, 2011
Lambar Labari: 2234379
Bangaren kasa da kasa, jamiyun siyasa da kungiyoyin addini na kare hakkin bil aama a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka kan harin da ‘yan adabar masarautar Bahrain suka kai kan masu gudanar da tarukan Ashura a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, daruruwan jamiyun siyasa da kungiyoyin addini na kare hakkin bil aama a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka kan harin da ‘yan adabar masarautar Bahrain suka kai kan masu gudanar da tarukan Ashura a fadin kasar wadda akasarin mutanen cikinta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ne.
A cikin bayani da gungun matasan 14 ga watan Fabrairu masu neman sauyi a kasar Bahrain ya fitar ya dora alhakin dukaknin abin da yake faruwa akasar na kai hare-hare kan masu gudanar da tarukan Ashura akan masarautar kasar, wadda ta dauki nauyin ‘yan bangare da suke kaddamar da wannan aiki na ta’addanci.
Gidan sarautar Bahrain wanda ke samun goyon baya kai tsaye daga masarautar kasar Saudiyya ya sha alwashin ci gaba da murkushe duk masu neman sauyi a kasar, inda yake ta kokarin ya yamar da zanga-zangar mutane ta mazhabanci da bangaranci an addini
Yanzu haka dai jamiyun siyasa da kungiyoyin addini na kare hakkin bil aama a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka kan harin da ‘yan adabar masarautar Bahrain suka kai kan masu gudanar da tarukan Ashura.
910671
captcha