IQNA

Mikewar Imam Hussain (AS) Na Gasgata Ayar Kur’ani Mai Tsarki

17:19 - December 05, 2011
Lambar Labari: 2234381
Bangaren kasa da kasa, mikewar da Imam Hussain (AS) ya yi tare da sauran iyalan gidan manzo da suke tare da shi da kuma sahabbansa, na gasgata ayar kur’ani mai tsarki da ke cewa, Allah ya umurci annabi Musa (AS) da ya tafi zuwa ga Fir’auna domin kuwa ya yi dagawa.

A wata zantawa da ta hada kamfanin dilalncin labaran iqna da kuma malamin addinin muslunci Hojjatol-Islam Basim Abidi, inda ya bayyana cewa mikewar da Imam Hussain (AS) ya yi tare da sauran iyalan gidan manzo da suke tare da shi da kuma sahabbansa, na gasgata ayar kur’ani mai tsarki da ke cewa, Allah ya umurci annabi Musa (AS) da ya tafi zuwa ga Fir’auna domin kuwa ya yi dagawa da shishigi ga Allah madaukakin sarki.
Ya ci gaba da cewa a lokacin da Yazid dan Mu’awiyya yake wakiltar shaidan da kuma mulki irin na fir’ananci a bayan kasa, Imam Hussain (AS) yana wakiltar manzon Allah ne, yana wakiltar dukaknin annabawan Allah ne a bayan kasa, shi ne ke rike da ragamar addini, saboda haka domin kiyaye martabar addini da wanzuwarsa kamar yadda Allah ya aiko amnzonsa da shi, hakan ne ya sanya ya ki mika kai ga fir’anan zamanisa Yazid dan Mu’awiyya Allah ya la’ance shi.
Shehin malamin ya kara da cewa, mikewar da Imam Hussain (AS) ya yi tare da sauran iyalan gidan manzo da suke tare da shi da kuma sahabbansa, ba ya ga gasgata ayar kur’ani mai tsarki da ke cewa, Allah ya umurci annabi Musa (AS) da ya tafi zuwa ga Fir’auna domin kuwa ya yi dagawa, a lokaci guda wannan yunkuri na Imam Hussain (AS) ‘yanci ne ga ‘yan adamtaka baki daya.
910242
captcha