Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Iraniyawa mazauna birnin Athen fadar mulkin kasar Girka suna gudanar da tarukan Ashura da suka saba yi a kowace shekara inda a yau ma suke yin zaman taro na ranar Tasu’a kamar yadda ake sa ran gobe idan Allah ya kai mu za a gudanar da tarukan Ashura.
Daga cikin malaman da suka gabar da jawabi wani malami ya ce a lokacin da Yazid dan Mu’awiyya yake wakiltar shaidan da kuma mulki irin na fir’ananci a bayan kasa, Imam Hussain (AS) yana wakiltar manzon Allah ne, yana wakiltar dukaknin annabawan Allah ne a bayan kasa, shi ne ke rike da ragamar addini, saboda haka domin kiyaye martabar addini da wanzuwarsa kamar yadda Allah ya aiko amnzonsa da shi, hakan ne ya sanya ya ki mika kai ga fir’anan zamanisa Yazid dan Mu’awiyya Allah ya la’ance shi.
Daruruwan Iraniyawa mazauna birnin Athen fadar mulkin kasar Girka suna gudanar da tarukan Ashura da suka saba yi a kowace shekara inda a yau ma suke yin zaman taro na ranar Tasu’a kafin gudanar da tarukan gobe na goma watan Muharram.
910915