Bangaren kasa da kasa: babban sakataren hukumar kula da kusanci a tsakanin mazahabobin musulunci dangane da harin da aka kai wa masu gudanar da juyayin ashura a Afganistan da aka kai masu a ranar goma ga watan Muhammaram ya fitar da wata sanarwa da a cikinta yake bayyana cewa wannna hari ne na dabbanci kuma suka yin Allah wadai da kai shi kuma wannan hari ne da ke nuni da aikin masu nuna bakar gaba da addini yan karan farautar ma'abuta girman kai na duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: babban sakataren hukumar kula da kusanci a tsakanin mazahabobin musulunci dangane da harin da aka kai wa masu gudanar da juyayin ashura a Afganistan da aka kai masu a ranar goma ga watan Muhammaram ya fitar da wata sanarwa da a cikinta yake bayyana cewa wannna hari ne na dabbanci kuma suka yin Allah wadai da kai shi kuma wannan hari ne da ke nuni da aikin masu nuna bakar gaba da addini yan karan farautar ma'abuta girman kai na duniya.A cikin wannan sanarwa ya bukaci malamai,shugabannin al'ummomi,masana da datijawa da jagorori da duk wani da zai iya bayar da gudummmuwarsa da dukan kabilu da al'ummomi da su hada kansu wajan tunkarar wannan makirci da kuma hadin kansu zai sa su tunkari duk wani makirci da ake kulla masu a yau a fili da kuma zaluntar su.
911764