IQNA

Sayyid Nasrullah Na Bin Salon Siyasa Ne Irin Na Imam Khomeni (RA) Da Shahid Sadr

16:55 - December 08, 2011
Lambar Labari: 2235211
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Hassan Nasrullah yana bin salon fikirar siyasa ne irin ta Imam Khomeni (RA) da kuma shahid Sadr a cikin lamurransa, musamman ma idana aka yi la’akari da yadda yake tabbatar da lamarin wiliyar malamai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin zantawar da ta hada shi da wakilin jami’ar Mustafa abirnin Beirut na kasar Lebanon Ja’afar Pishe ya bayyana cewa, Sayyid Hassan Nasrullah yana bin salon fikirar siyasa ne irin ta Imam Khomeni (RA) da kuma shahid Sadr a cikin lamurransa, musamman ma idana aka yi la’akari da yadda yake tabbatar da lamarin wiliyar malamai masu tsoron Allah da bin tafarkin Imam Huja Allah ya gagauta bayyanarsa.
Babban sakataren kungiyar ta gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, sadaukantarwar da Imam Hussain (AS) da iyalan gidan amnzon Allah suka yi a Karbala, na da babban tasiri wajen kafuwar gwagwarmaya da zalunci a kasar Lebanon daga ciki kuwa har da kungiyar ta Hizbullah.
Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban dubabn mutane da suka taru a hubbaren Sayyid Abbas Musawi, wanda shi ne sakataren kungiyar ta Hizbullah da ya yi shahada sakamakon harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kansa tare da iyalansa a lokacin da suke tafiya a mota.
Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, sadaukantarwar da Imam Hussain (AS) da iyalan gidan amnzon Allah suka yi a Karbala, na da babban tasiri wajen kafuwar gwagwarmaya da zalunci a kasar.
910724

captcha